Wannan lamari da majiyoyin tsaro suka tabbatar sun bayyana shi a matsayin babban koma-baya ga tsarin shugabancin ƙungiyar.

Majiyoyin sun shaida cewa hare-haren, da aka kai a cikin kwanaki uku zuwa huɗu da suka gabata a yankin yammacin Dogon Chukun, sun yi nasarar tarwatsa wani taron manyan ‘yan ta’addar ƙungiyar.

An ce daga cikin waɗanda aka kashe akwai mambobin majalisar shura guda uku, da kuma wasu manyan kwamandojin yaƙi biyu da ake kira “Munzirs”, tare da wasu mayaƙa da dama da ke aiki a matsayin masu tsaro.

Majiyoyin sun ƙara da cewa wannan hari ya girgiza tsarin jagorancin ƙungiyar, kasancewar majalisar shura na taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufofi da yanke manyan shawarwari.

Haka kuma, an ruwaito cewa wani babban jigo a cikin ƙungiyar, wanda aka bayyana da suna Yaa Bashir, ya samu mummunan rauni a ƙafarsa, yayin da wani mayaƙi ɗan ƙetare mai suna Abu Khalid, wanda ake zargin ɗan ƙasar Larabawa ne, shi ma ya jikkata ƙwarai.

Ana ci gaba da tantance cikakken tasirin harin, tare da ƙoƙarin gano asalin sauran waɗanda abin ya shafa.

Majiyoyin tsaro sun jaddada cewa wannan farmaki wani ɓangare ne na ci gaba da ayyukan rundunar Operation Haɗin Kai na daƙile ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.