Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2027

A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce ya zama ɗantakarar jam'iyyar ne bayan samun kuri’un amincewa daga wakilan jam'iyyar a yayin zaɓen fitar da gwani da aka gudanar a yau Alhamis.

Ta ce an gudanar da zaɓen fitar da gwanin ne a gaban jami’an hukumar zaɓe ta INEC.

Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen Hon. Hafiz Ibrahim Kawu, ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana.