Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya musanta rahotannin da ke cewa yana shirin sauya sunan Najeriya tare da soke Shari’ar Musulunci a Arewacin kasar nan.

wannan na cikin sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga ya fitar.

Sanarwar ta ce babu gaskiya a rahotannin da ke yawo cewa Tinubu na shirin gabatar da kudirin gyaran kundin tsarin mulki domin sauya sunan kasar nan zuwa United States of Nigeria.

Ya ce wasu ‘yan siyasa ne ke yada rahotannin karya domin haddasa rikici da tayar da hankalin jama’a gabanin babban zaben 2027.

Fadar shugaban kasa ta kuma bukaci ‘yan Najeriya su yi hattara da rahotannin karya da ka iya haddasa rarrabuwar kawuna a tsakanin al’umma.