Shugaban ƙasar amurika Donald Trump ya sanar da cewa tattaunawar zaman lafiya da Iran ta kai matakin karshe, inda ya ba wa kasar wa’adin kwanaki biyu zuwa uku kacal domin ta amince da yarjejeniyar, ko kuma ta fuskanci mummunan harin soja.
Wannan sanarwa ta zo ne bayan matakin da Trump ya ɗauka na dakatar da wani babban harin bam da Amurka ta shirya kai wa Iran.
Shugaban ya bayyana cewa ya janye harin ne bayan buƙata da shawara daga shugabannin ƙasashen Larabawa na yankin Gulf, waɗanda ke ganin akwai alamun samun maslaha.
Trump ya jaddada cewa lokaci yana ƙure wa Iran, yana mai barazanar cewa hari na gaba da zai kai mata zai kasance mafi muni idan har ba a cimma yarjejeniyar ba kafin ƙarshen mako.