Wasu majiyoyi biyu ne suka tabbatar da afkuwar harin ga kamfanin dillancin labaran Faransa, a cewar wasu masu yaƙi da ayyukan mayaƙan da kuma jami’in ƙungiyar masunta da ke yankin sun ce tun a ranar litinin ɗin da ta gabata mayaƙan suka kai hari a yankin Mafa inda suka kashe masunta 27, sai kuma a yankin Dikwa da suka kashe masu sarar itatuwa shida.


Shugaban ƙungiyar masu kamun kifin na Maidugurin Abdullahi Sani ya ce matsuntan na kan hanyar su ta dawowa daga aiki lokacin da maharan suka afka musu.


Gabanin nan, mayaƙan Boko Haram sun harɓe masu sarar itatuwa shida lokacin da suke karɓar itace a cikin wani daji da ke wajen ƙauyen Malam Maja a yankin na Dikwa.


Wannan na zuwa ne, makonni biyu kacal bayan mayaƙan sun kashe masu sarar itatuwa 18 a wani daji da ke kusa da ƙauyen Abaram a garin Bama.


Hakan na nuni da irin yadda ayyukan ƙungiyar Boko Haram ke ci gaba da dawowa, bayan saukin da aka samu a shekarun baya, bayan mummunar ɓarnar da hare-haren mayakan yayiwa al’ummar Borno da kewaye.