Fitaccen lauya mai kare haƙƙin bil’adama Nuhu Hamza Dantani ya bayyana cewa ya gana da Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya Olayunji Disu domin tattauna batutuwan da suka shafi zargin take haƙƙin jama’a da ake yi wa wasu jami’an ‘yan sanda.
Dantani ya wallafa bayanin ganawar a shafinsa na Facebook ranar Juma’a, inda ya ce a yayin tattaunawar ya yi zargin cewa wasu jami’an ‘yan sanda na tsare mutane ba bisa ƙa’ida ba, tare da cin zarafi ta hanyar duka da kuma barazana.
Haka kuma an tattauna batun yadda za a daƙile matsalar faɗan daba a Jihar Kano, tare da neman hanyoyin gudanar da bincike kan kisan wasu mutane biyar da aka ruwaito a makonnan da suka gabata.
A nasa ɓangaren, IGP ya tabbatar da cewa rundunar za ta ɗauki mataki kan duk wani jami’i da aka tabbatar da laifin take haƙƙin ɗan adam, tare da jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin tsare mutane yadda doka ta tanada a cikin rundunar Nigeria Police Force.
Ya kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin kisan wani ɗan gwagwarmaya mai suna Dadiyata.
A ƙarshe, ya buƙaci duk masu korafi kan cin zarafi ko tsarewa ba bisa doka ba da su kai rahotonsu ga sashen karɓar ƙorafe-ƙorafe na ‘yan sanda (CRU) domin bincike da daukar mataki.