Attajirin ɗan kasuwa Femi Otedola, ya bayyana shirin sa na saka hannun jarin dala miliyan 100 a matatar mai ta Dangote.


Otedola ya bayyana hakan ne bayan wata ziyara da ya kai matatar a ranar Laraba.


Ya ce hannun jarin na daga cikin shirin tara dala biliyan biyu da matatar Dangote ke yi daga hannun masu zuba jari masu zaman kansu kafin fitar da hannun jarin kamfanin a kasuwa.


A cewarsa, ya tattauna da Aliko Dangote sau da dama, inda ya nemi a ware masa hannun jari na dala miliyan 100 a cikin tsarin sayar da hannun jarin kamfanin.


Otedola ya bayyana cewa daya daga cikin dalilan da suka sa ya sayar da hannun jarinsa a kamfanin Geregu Power shi ne domin ya samu damar zuba kudin a matatar Dangote.


Tun a shekarar 2025 Aliko Dangote ya bayyana cewa matatar na shirin sayar da kashi 10 cikin 100 na hannun jarin ta a kasuwar hada-hadar hannayen jari.


Rahotanni sun nuna cewa ana hasashen darajar matatar Dangote za ta iya kaiwa dala biliyan 50 idan aka kammala shirin fitar da hannun jarin.