Wani matashi mai suna Abdulmutallab Yusuf ya rasa ransa, yayin da wasu mutum 12 suka jikkata bayan rikicin da ya ɓarke sakamakon zaɓen fid-da-gwani na jam’iyyar APC a Mazaɓar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa Nasiru Idris ne ya lashe zaɓen bayan samun ƙuri’u 853, yayin da abokin takarar sa Bashir Zango ya samu ƙuri’u 213.
Rahotanni sun ce rikicin ya fara tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu bayan kammala zaɓen, lamarin da ya rikide zuwa tashin hankali a wasu unguwannin yankin.
Malam Yusuf Abdullahi, mahaifin mamacin, ya bayyana cewa yana gida lokacin da aka sanar da shi cewa an harbi ɗansa a ƙirji. Ya ce da ya isa asibiti, sai ya tarar cewa Abdulmutallab ya riga ya rasu.
A cewarsa, marigayin ba ya cikin harkokin bangar siyasa, domin yana taimaka masa wajen sayar da magungunan gargajiya a kasuwannin da ke kusa da Zariya.
Shi ma wani da ya samu raunuka, Lukman Garba, ya ce wasu matasa sun tare hanya a yankin Unguwar Gwado inda suka kai musu hari da makamai, lamarin da ya janyo jikkatar mutane da dama daga yankunan Muchiya da Cikaji.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce ba zai iya yin bayani kan lamarin ba a lokacin saboda yana cikin wani taro.