Rundunar yansandan jihar Kano ta ce ta samu nasarar kame fiye da mutane 200, da ake zargi da fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka, a faɗin jihar Kano.
Kwamishinan yansandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori, shine ya sanar da haka ya yi wani taron manema labarai da aka gudanar a shelkwatar rundunar.
Haka kuma ya ce rundunar ta samu nasarar kuɓutar da mutane uku da akayi garkuwa da su, tare da kama mutum 5 daga cikin masu garkuwar.
Rundunar tace ta samu wadannan nasarori ne a ayyuka na musamman da ta gudanar a watan Afrilun da ya gabata a sassa daban-daban.