Wasu ‘yan bindiga sun yi fashin raguna 11 daga wasu ‘yan kasuwar Karamar Hukumar Ajingi a Nan Kano, yayin da suke hanyar su ta zuwa jihar Kogi domin cin kasuwar Babbar Sallah.
Daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa, Alhaji Hamisu Abdu Sakalawa, ya shaida wa Arewa Updates, cewa lamarin ya faru ne cikin dare a garin Dakatsalle, a karamar hukumar Bebeji.
Hamisu ya ce sun tsaya jiran motar da za ta dauke su zuwa garin Ankwa da ke Jihar Kogi, sai ga maharan sun zo a cikin mota ɗauke da bindigu.
Yace ayan sun yi harbe-harbe a iska, sai su ka umarci su kwanta su rufe idanun su, daga nan suka kwashe ragunan suka gudu da su.
Ya kara da cewa sun kai korafi a ofishin ‘yan sanda na Dakatsalle bayan faruwar lamarin.