Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano ta rantsar da ɗalibai sama da 5,000, wanda suka fara daukar darasi domin a zangon karatu na shekarar 2025/2026.


A yayin bikin da aka gudanar ranar Laraba, shugaban kwalejin, Dakta Abubakar Umar Farouk, wanda Injiniya Dakta Ibrahim Usman Aikawa ya wakilta, ya bukaci sabbin ɗaliban da su rungumi kyawawan ɗabi’u da manufofin makarantar da suka haɗa da gaskiya, ƙwarewa, ladabi, kirkire-kirkire da kuma mutunta juna.


Ya kuma ƙarfafa musu gwiwa da su mayar da hankali wajen karatun su tare da amfani da lokacin su yadda ya kamata domin cimma nasara a rayuwa.


A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na kwalejin, Auwal Ismail Bagwai, ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa jami’an makarantar sun gargadi ɗaliban kan aikata satar amsa yayin jarabawa da kuma sanya tufafin da ba su dace da tarbiyya ba.


Shi ma magatakardar kwalejin, Mukhtar Ibrahim Bello, ya taya ɗaliban murnar samun gurbin karatu tare da jan hankalin su da su kasance jakadu nagari ga kwalejin a duk inda suka samu kan su.