Hukumar Zabe ta kasa INEC reshen Jihar Kano Za Ta Gudanar da Zaɓen Cike Gurbi na dan majalisar wakilai a Ƙananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa.
Hakan ya biyo bayan rasuwar dan majalisar yankin a kwanakin baya.
Hukumar ta sanar da hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana a shelkwatar hukumar da ke Kano.
Shugaban hukumar zaɓe ta jihar Kano, Abdu A. Zango, ya ce zaɓen zai gudana a ranar 20 ga watan gobe kamar yadda hukumar ta tsara.
Wakilinmu Rabiu Ahmad Kofar Mazugal ya rawaito mana cewa tuni hukumar ta fara dukkan shirye-shiryen da suka dace, ciki har da ɗaukar ma’aikatan wucin gadi tare da tuntubar masu ruwa da tsaki da jami’an tsaro domin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.