Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta sake gano wani gagarumin kamu na ƙwayoyi da darajarsu ta kai naira biliyan 480, tare da kama wasu ƴan asalin ƙasar Mexico da hannu a cikin wannan sana’ar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ya fitar a larabaci, an bayyana cewa NDLEA ta tarwatsa wata gungiyar masu safarar ƙwayoyi tsakanin Najeriya da Mexico.

Hukumar ta ce ta gano wani haramtaccen kamfani na sarrafa ƙwayoyi, wanda ta bayyana a matsayin mafi girma da ta taɓa ganowa, a yankin Ijebu na jihar Ogun.

Baya ga gano kamfanin, NDLEA ta kama jagoran gungiyar masu safarar ƙwayoyin, tare da wasu ƙwararrun ƴan asalin Mexico, da kuma wasu mutane shida da ke taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu na haram.

Shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya (Rtd.), ya ce wannan gagarumar nasara ta samu ne bayan shafe tsawon watanni ana bibiya tare da tattara bayanan sirri, inda daga ƙarshe aka ƙaddamar da samame a jihohin Lagos da Ogun.

Wannan nasara ta zo ne ƙasa da makonni biyu bayan wata gagarumar aiki da NDLEA ta yi tare da haɗin gwiwar hukumomin Amurka, Faransa, Girka, da Switzerland, inda aka tarwatsa wasu gungun masu safarar ƙwayoyi na ƙasa da ƙasa