Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ta sallami wani lauya na gwamnati, Mustapha Nura Muhammad, bayan an same shi da laifin bayar da bayanan ƙarya tare da amfani da sunaye da sa hannun manyan lauyoyin ma’aikatar ba tare da izini ba.

Wata sanarwa daga Mataimakin Kwamishinan Shari’a kan Yada Labarai, Dr. Abubakar Tijjani Ibrahim, ta bayyana cewa Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Kano ta amince da hukuncin ne bayan nazarin rahoton kwamitin ladabtarwa a zamanta na 1 ga Afrilu, 2026.

Bincike ya nuna cewa lauyan ya fitar da shawarwarin shari’a ta hanyar amfani da sa hannun manyan jami’ai, lamarin da ya haifar da kama da tsare wani mutum da ba shi da alaka da shari’ar.

Ma’aikatar ta ce an bi duk matakan ladabtarwa, inda aka ba shi damar kare kansa kafin a kai ga dakatarwa da kuma mika shawarwarin korarsa ga kwamitin da ke kula da manyan ma’aikata, wanda daga bisani ya amince da matakin korar sa bisa dokokin aikin gwamnati.