Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar duba yadda aikin sake gina hanyoyin cikin birni ke gudana a yankin Farm Centre da ke cikin birnin Kano.
Ziyarar wadda ta gudana a ranar Laraba, 20 ga watan Mayu 2026, na daga cikin matakan tabbatar da inganci da kuma saurin kammala ayyukan more rayuwa da Gwamnatin jihar ke aiwatarwa domin inganta zirga-zirgar al’umma.
A yayin ziyarar Gwamnan ya jaddada kudirin Gwamnatinsa na cigaba da bunkasa ababen more rayuwa musamman hanyoyi, domin saukaka harkokin sufuri da kasuwanci a fadin jihar.