Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarun haɗin gwiwarta na Joint Task Force tare da Operation Hadin Kai sun samu nasarar daƙile wani hari mai ƙarfi da aka shirya kai wa a yankin Arewa maso Gabashin ƙasar, yayin ayyukan tsaro da suke gudanarwa a yankin.

Rundunar ta ce sojojin nata sun kuma kama wasu da ake zargi da taimaka wa masu tayar da ƙayar baya da kuma ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.

A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, harin da dakarun da ke sansanin FOB Gajibo suka daƙile, ana zargin cewa mayaƙan Boko Haram/ISWAP ne suka shirya kai harin inda suka taho da babura daga fannoni daban-daban.

Sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa ta amfani da makamai masu nauyi, abin da ya tilasta wa maharan ja da baya.

Rundunar ta ce sojojijin sun kuma ƙwace harsasai da wasu kayan yaƙi, ba tare da asarar rai a ɓangaren sojojin ba..

Sanarwar ta kuma ce wani matashi ɗan shekara 17 da ke da alaƙa da iyalan ƴanbindigar ya tsere daga sansanin su da ke Dutsen Mandara, inda daga baya ya miƙa kansa ga sojoji a kan hanyar Gwoza zuwa Limankara.