Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani na Nijeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya janye takararsa daga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC domin neman kujerar gwamnan Jihar Gombe. Ya bayyana hakan a wata sanarwa da lauyansa, Barista Ibrahim M. Attahir, ya fitar ranar Talata.


Pantami ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki da kuma nazarin abubuwan da suka faru game da zaɓen. Ya danganta janyewar da zargin take Dokar Zaɓe ta 2026 da rashin gaskiya a tsarin zaɓen cikin gida na jam’iyyar.


Ya kara da cewa duk da ya bi dukkan ka’idojin APC kuma ya amsa kiran matasa, mata da shugabannin al’umma da suka buƙace shi ya tsaya takara, sai aka hana shi samun muhimman bayanai da ake buƙata don gudanar da sahihin zaɓe.


Lauyoyinsa sun aika wasiƙu zuwa ga shugabannin APC suna neman haske kan hanyoyin zaɓe, tantance wakilai, cibiyoyin tattara sakamako da sauran bayanai, amma ba a ba su amsa ba.


Pantami ya kuma nuna damuwa kan yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani na ‘yan majalisa a ranakun 16 da 18 ga Mayu, inda aka ware mambobin jam’iyyar na ƙasa daga tsarin duk da an sanar da sakamako.


Ya ce ƙarfinsa a siyasa ya fito ne daga goyon bayan matasa da mata, kuma irin waɗannan kura-kurai sun saɓa wa dimokuradiyya da Dokar Zaɓe ta 2026.


Pantami ya bayyana cewa shi kaɗai ne daga cikin masu neman takarar gwamna na APC ya aika wakili zuwa taron yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan sanda suka shirya a Gombe ranar 14 ga Mayu, kuma wakilinsa shi kaɗai ya sanya hannu kan yarjejeniyar.


Ya ce janyewarsa daga zaɓen da aka shirya ranar 21 ga Mayu, zanga-zangar lumana ce don kare dimokuradiyya, bin doka, da tabbatar da sahihin zaɓe.


Sanarwar ta yaba wa magoya bayansa, musamman matasa da suka tara kuɗi daga Naira dubu biyar zuwa miliyan huɗu don sayen fom ɗin nuna sha’awarsa.


Pantami ya buƙaci dukkan magoya bayan kungiyar Pantamiyya su kasance masu bin doka da zaman lafiya, kuma zai sanar da matakai na gaba nan ba da jimawa ba. Ya jaddada kudirinsu na ci gaba da fafutukar samar da shugabanci nagari a Gombe da Najeriya gaba ɗaya ta hanyar lumana da bin tsarin dimokuradiyya.