Tsohon ministan sufuri kuma ɗan takarar gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar APC, Sa'idu Ahmed Alkali, ya sanar da janye kansa daga shiga zaɓen fidda gwani na gwamna da jam’iyyar za ta gudanar ranar 21 ga watan Mayun 2026.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Umar Alkali Jibrin ya fitar, Sanata Alƙali ya ce ya ɗauki matakin ne saboda abin da ya kira rashin gaskiya da karya dokokin zaɓe a jihar.
Sanarwar ta bayyana cewa Alƙali ya cika dukkan sharuɗɗan shiga takarar gwamna, ciki har da sayen fom ɗin nuna sha’awa da na tsayawa takara tare da wuce tantancewar da jam’iyyar ta gudanar. Sai dai ya ce yadda aka gudanar da zaɓukan fidda gwani na majalisar wakilai da sanatoci a yankunan Gombe/Kwami/Funakaye, Billiri/Balanga da Gombe ta Tsakiya a ranakun 16 da 18 ga watan Mayu ya sa ya rasa ƙwarin gwiwa kan sahihancin tsarin zaɓen.
A cewarsa, "zaɓukan sun gudana cikin maguɗi, rashin gaskiya da kuma karya sashe na 86 na dokar zaɓe ta 2026, wanda ya tanadi cewa dole ne a gudanar da zaɓen fidda gwani bisa ƙa’idojin jam’iyya."
Ya ce an gudanar da zaɓukan ba tare da isassun kayan aiki da jami’an zaɓe da masu sa ido da sauran shirye-shiryen da suka dace ba, lamarin da ya nuna cewa babu adalci ko gaskiya a tsarin.
Duk da janyewar tasa daga takarar, Sanata Alƙali ya tabbatar da ci gaba da biyayya da goyon bayansa ga jam’iyyar APC domin samun nasara a babban zaɓen shekarar 2027.