Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya, FAAN ta ɗauki tsauraran matakan kariya a dukkan filayen jiragen saman ƙasa da ƙasa domin dakile yaduwar cutar Ebola bayan bullarta a wasu sassan Afirka ta Tsakiya.
A wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a da Kare Haƙƙin Fasinjoji na hukumar, Henry Agbebire, ya fitar, FAAN ta ce tana aiki tare da cibiyar dakile yaduwar cututtuka, Hukumar Kula da Lafiyar Tashoshin Jiragen Ruwa da Sama, da sauran hukumomi domin ƙarfafa sa ido kan fasinjojin da ke shigowa Najeriya, musamman daga yankunan da ake fuskantar haɗarin cutar.
Hukumar ta bayyana cewa ana tantance fasinjoji domin gano alamomin cutar Ebola, kuma duk wanda ake zargi da kamuwa da cutar za a killace shi tare da yi masa ƙarin binciken lafiya bisa ƙa’idojin lafiya na ƙasa da ƙasa.
FAAN ta kuma ce ta ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin da abin ya shafa, tare da wayar da kan ma’aikata da inganta matakan gaggawa domin tabbatar da ɗaukar mataki cikin sauri idan bukatar hakan ta taso