Tsohon ministan tsaro, Theophilus Danjuma, ya bayar da gudunmawar Naira biliyan 3 yayin ƙaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban ƙasa, Yakubu Gowon mai suna “My Life of Duty and Allegiance” da aka gudanar a Abuja ranar Talata.

Haka kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya sayi kwafi 25 na littafin kan Naira miliyan 500 ta hannun wakilinsa, Mansur Ahmed.

Shugaban BUA Group, Abdul Samad Rabiu, shi ma ya sayi kwafi na littafin da kudinsu ya kai naira miliyan 25.

Rahotanni sun bayyana cewa Danjuma ya kuma umarci a saya tare da rabawa dakunan karatu na jami’o’i 20 da suka bai wa Gowon digirin girmamawa.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya wakilci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen taron da ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, jakadu da manyan hafsoshin soja.

A jawabinsa, Danjuma ya yabawa Gowon kan rawar da ya taka wajen haɗa kan Najeriya bayan yaƙin basasa, musamman ta hanyar manufarsa wadda ya ce ta taimaka wajen sulhunta ƙasa da dawo da zaman lafiya bayan yaƙin