Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yaba wa al’ummar Hausawa bisa muhimmiyar rawar da suke takawa wajen ƙarfafa haɗin kai da bunƙasa Najeriya.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake taya al’ummar Hausawa murnar Ranar Hausa, wadda ake gudanarwa a masarautar Daura mai tarihi.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya ce harshen Hausa ya samu gagarumar bunƙasa, inda ya zama ɗaya daga cikin muhimman harsunan sadarwa da kasuwanci a sassa daban-daban na duniya.
Ya ce al’ummar Hausawa na ci gaba da bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen ci gaban Najeriya da kuma ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin al’ummomin ƙasar.
Shugaban Ƙasar ya taya ɗaukacin al’ummar Hausawa murnar wannan rana, tare da yi musu fatan alheri da samun nasara yayin gudanar da bikin Ranar Hausa.