Babban Darakta na National Institute for Cancer Research and Treatment (NICRAT), Farfesa Usman Malami Aliyu, ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da gina babbar Cibiyar Bincike da Maganin Cutar Daji ta Ƙasa, wadda za a kashe kusan Naira biliyan 302.3 wajen gina ta da kuma samar mata da kayan aiki.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na NICRAT, Hassan Zaggi, ya fitar a Abuja, Farfesa Malami ya ce amincewar ta biyo bayan sanarwar da Ministan Lafiya da Jinƙai na Jama’a mai kula da ma’aikatar, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya yi a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) na makon da ya gabata.
An tsara kammala aikin cibiyar cikin watanni 36.
Farfesa Malami ya ce amincewar na nuna kulawa da damuwar gwamnatin Shugaba Tinubu game da lafiyar ’yan Najeriya da jin daɗinsu.
Ya ce aikin zai kuma tabbatar da ƙudurin gwamnatin wajen aiwatar da manyan ayyukan da za su inganta rayuwar ’yan ƙasa.
A cewarsa, cibiyar za ta iya mayar da Najeriya wata muhimmiyar cibiyar kula da cutar daji da bincike a Afirka da ma duniya baki ɗaya.
Ya ce cibiyar za ta ƙarfafa bincike, magani, kirkire-kirkire da horas da ma’aikatan lafiya, tare da samar da ingantattun ayyukan kula da masu fama da cutar daji bisa ƙa’idojin duniya.
Farfesa Malami ya kuma bayyana cewa amincewar na daga cikin matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka wajen ƙara yawan cibiyoyin kula da cutar daji a ƙasar. Ya ce an riga an kammala wasu cibiyoyi uku a Katsina, Benin da Enugu.
Ya tuna cewa tsawon shekaru cutar daji ta kasance babbar barazana ga ’yan Najeriya, musamman saboda ƙarancin cibiyoyin gano cutar da wuri, magani da bincike.
A cewarsa, wannan matsala ta sa mutane da dama ke kasa gano cutar da wuri ko samun maganin da ya dace cikin sauƙi da farashi mai sauƙi.
Farfesa Malami ya bayyana amincewar Shugaban Ƙasa da aikin cibiyar a matsayin sabon sauyi mai muhimmanci, musamman saboda za ta taimaka wajen rage yawan ’yan Najeriya da ke fita ƙasashen waje domin neman ingantaccen maganin cutar daji.
Ya ce Najeriya na kashe miliyoyin daloli a kowace shekara saboda tafiyar marasa lafiya zuwa ƙasashen waje domin bincike da maganin cutar daji.
A lokaci guda, ya ce cibiyar za ta iya mayar da Najeriya wurin da mutane daga wasu ƙasashen Afirka da sauran sassan duniya za su riƙa zuwa domin neman magani da gudanar da bincike, wanda hakan zai taimaka wajen ƙara samun kuɗaɗen waje ga ƙasar.
Ya ƙara da cewa cibiyar za ta samar da yanayi da kayan aiki na zamani da za su ba ƙwararrun likitocin cutar daji damar gudanar da bincike da samar da sabbin hanyoyin magance cutar.
Bugu da ƙari, cibiyar za ta kasance wajen horaswa da ƙara ilimin ƙwararrun likitocin cutar daji da masu bincike daga Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.
Farfesa Malami ya ce aikin zai kuma taimaka wajen samar da ƙwararrun ma’aikatan kula da cutar daji, inganta manufofin kiwon lafiya bisa hujjojin bincike, ƙarfafa amfani da fasaha wajen kula da marasa lafiya da kuma bunƙasa haɗin gwiwa tsakanin cibiyoyin lafiya na cikin gida da na ƙasashen waje.
Ya ce amincewar Shugaban Ƙasar za ta kafa tubalin inganta tsarin kiwon lafiya da zai kasance cikin shiri wajen tinkarar sauye-sauyen buƙatun kiwon lafiyar al’ummar Najeriya mai ƙaruwa.
Farfesa Malami ya kuma yaba wa Ministan Lafiya da Jinƙai na Jama’a mai kula da ma’aikatar, Farfesa Muhammad Ali Pate, bisa jagorancinsa da ƙoƙarinsa na sauya fasalin fannin kiwon lafiya.
Haka kuma ya yaba wa Ministan Ƙasa na Lafiya da Jinƙai na Jama’a, Dr Iziaq Adekunle Salako, bisa dagewarsa da goyon bayansa wajen ganin an tabbatar da wannan muhimmin shiri.
Ya ce mahukunta da ma’aikatan NICRAT sun ƙuduri aniyar yin aiki tuƙuru domin ganin aikin ya cika manufofin Renewed Hope Agenda tare da samar da ingantaccen tsarin kula da masu fama da cutar daji a Najeriya.