Gwamnatin Tarayya ta ce tana duba yiwuwar soke yarjejeniyar rangwame ta aikin hanyar Benin–Asaba saboda zargin gazawar kamfanin da aka bai wa aikin da kuma tafiyar hawainiyar da ake yi wajen kammala aikin.
Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar duba aikin a birnin Benin, babban birnin Jihar Edo.
Ziyarar ministan zuwa hanyar Benin–Agbor bypass ta biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu, bayan wata zanga-zangar da matasan Edo suka gudanar a baya kan abin da suka bayyana a matsayin rashin kyakkyawan gudanar da aikin.
Matasan sun ce jinkirin da ake samu wajen kammala aikin ya jefa masu amfani da hanyar cikin matsananciyar wahala.
Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, da wasu ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ne suka raka ministan yayin ziyarar duba aikin.
A lokacin binciken, Sanata Umahi ya nuna rashin gamsuwa da irin aikin da kamfanin da aka bai wa aikin ya gudanar, musamman wajen inganci da saurin aikin.
Ministan ya ce idan ba a samu sauyi cikin gaggawa ba, gwamnatin tarayya ba za ta rasa wani zaɓi ba face soke kwangilar tare da bai wa wani kamfani da ya fi ƙwarewa aikin.
Ya ce gwamnati na buƙatar ganin aikin yana tafiya yadda ya kamata domin rage wahalhalun da masu amfani da hanyar ke fuskanta da kuma tabbatar da kammala muhimmin aikin cikin lokaci.