Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Rundunar Sojin Najeriya, ’Yan Sandan Najeriya, Hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro da leƙen asiri da abin ya shafa da su ƙaddamar da aikin ceto cikin gaggawa domin kuɓutar da mutanen da aka sace a wani sabon harin satar mutane da yawa a Jihar Neja.

A cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana matuƙar ɓacin ransa kan sacewa da kashe fararen hula da wasu miyagu suka yi a jihar.

Shugaban ya ce waɗanda suka kai harin kan mutanen da ba su da makami “makiyan zaman lafiya ne da makiyan bil’adama”, kuma ba za a bar su su tafi haka nan ba tare da an hukunta su ba.

Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda aka kashe, tare da addu’ar Allah Ya jikansu da rahama, Ya kuma ba iyalansu ƙarfin zuciyar jure wannan babban rashi.

Tinubu ya ce gwamnati da al’ummar Najeriya gaba ɗaya suna tare da iyalan waɗanda lamarin ya shafa, yana mai cewa ba za a huta ba har sai an dawo da dukkan waɗanda aka yi garkuwa da su cikin aminci.

Shugaban Ƙasa ya umarci shugabannin hukumomin tsaro da su riƙa ba shi cikakken bayani akai-akai kan ci gaban aikin ceto har zuwa lokacin da za a gano tare da dawo da dukkan mutanen da aka sace.

Ya ce:

“Ta’addanci ba zai tsoratar da Najeriya ba. Za mu kare mutanenmu, mu kare al’ummominmu, kuma mu tabbatar da mutuncin rayuwar ɗan Adam.”

Tinubu ya kuma miƙa addu’o’insa ga al’ummar Jihar Neja a wannan mawuyacin lokaci, tare da tabbatar da cewa gwamnatin tarayya tana tsaye tare da gwamnatin jihar.

Ya ce gwamnatin tarayya za ta samar da dukkan tallafin da ake buƙata domin taimakawa wajen farfaɗowa, agajin gaggawa da kuma ƙara ƙarfafa tsaro a jihar.