Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, ya buƙaci ƙasashen Afirka da su ƙarfafa masana’antunsu domin samar da guraben ayyukan yi, bunƙasa tattalin arziki da kuma inganta tsaro a nahiyar.
Jonathan ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da lacca ta kammala karatu ga ɗaliban National Defence College Course 34, mai taken “Harnessing Industrial Capacity for Inclusive Growth and Regional Stability in Africa”.
Ya ce yayin da miliyoyin matasa a Afirka ke shiga kasuwar ƙwadago a kowace shekara, ƙarancin masana’antu a nahiyar ya daina kasancewa matsalar tattalin arziki kawai, domin yana ƙara zama barazana ga samar da ayyukan yi, zaman lafiyar al’umma da tsaro.
Tsohon shugaban ya ce tun bayan fara juyin juya halin masana’antu a ƙarshen ƙarni na 18, duniya ta samu gagarumin sauyi a fannonin masana’antu, fasaha da bunƙasar tattalin arziki.
Sai dai ya ce Afirka ta kasa yin daidai da wannan ci gaba, inda ƙarancin masana’antunta ke ci gaba da takaita bunƙasar tattalin arziki, samar da ayyukan yi da ci gaba.
Jonathan ya jaddada cewa gibin masana’antu da Afirka ke fama da shi ya wuce matsalar tattalin arziki, domin yanzu ya zama batun tsaro mai muhimmanci.
Ya ce rashin aikin yi da ƙarancin damar samun abin yi na samar da yanayin da zai iya haifar da yaɗuwar tsattsauran ra’ayi da tashin hankali, aikata manyan laifuka cikin tsari da kuma ƙaura ba bisa ƙa’ida ba.
Tsohon shugaban ya ce matuƙar ƙasashen Afirka ba su samar da masana’antu masu gogayya da za su samar da ayyukan yi, bunƙasa ƙwarewar cikin gida da faɗaɗa damar tattalin arziki ba, ƙoƙarin tabbatar da dorewar zaman lafiya, kwanciyar hankali a yankuna da kuma ci gaban da ya shafi kowa a nahiyar zai ci gaba da fuskantar manyan ƙalubale.
Ya ƙara jaddada cewa ƙarfafa masana’antu zai taimaka wajen bai wa matasa damar dogaro da kansu, rage matsin tattalin arziki da kuma magance wasu daga cikin abubuwan da ke haifar da rashin tsaro a sassa daban-daban na nahiyar.