Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan, abokan arziki da abokan aikin fitaccen jarumin Nollywood, mai shirya fina-finai kuma marubucin wasan kwaikwayo, Taiwo Hassan, wanda aka fi sani da Ogogo, bayan rasuwarsa.
A cikin wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana marigayi Hassan a matsayin ƙwararren ɗan fasaha wanda aikinsa ya shafe shekaru da dama, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa wasan kwaikwayo da fina-finan harshen Yarbanci da kuma sinimar Najeriya.
Shugaban ya ce ta hanyar irin salon wasansa na musamman, ƙwarewarsa a gaban kyamara da kuma jajircewarsa wajen aikinsa, Ogogo ya nishaɗantar da tsararraki na ’yan Najeriya tare da tallata kyawun al’adun Yarbawa da ɗimbin al’adun Najeriya.
Tinubu ya ce ayyukan da Ogogo ya bari za su ci gaba da kasancewa wani muhimmin ɓangare na tarihin al’adun Najeriya. Ya ƙara da cewa irin gudunmawar da ya bayar wajen horar da matasa masu tasowa a masana’antar nishaɗi ta ƙara tabbatar da irin gagarumar gadon da ya bari.
Shugaban Ƙasar ya ce:
“Alhaji Taiwo Hassan ƙwararren ɗan fasaha ne wanda ya yi amfani da baiwarsa wajen ba da labaran Najeriya, kiyaye al’adunmu da nishaɗantar da jama’a a gida da ƙasashen waje.
“Rasuwarsa babban rashi ne ga iyalansa, masana’antar fina-finan Yarbanci, Nollywood da kuma dukkanin al’ummar masu fasaha a Najeriya.
“A madadin gwamnatin tarayya, ina miƙa ta’aziyyata ga iyalansa, abokan aikinsa, abokansa da miliyoyin masoyansa. Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jikansa da rahama, Ya ba iyalansa da sauran waɗanda wannan rashi ya shafa ƙarfin zuciyar jure wannan babban rashi.”
Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci ’yan masana’antar shirya fina-finai da sauran ’yan Najeriya da su girmama ƙwaƙwalwar Ogogo ta hanyar kiyaye tare da bunƙasa kyawawan al’adu da ɗabi’un fasaha da ya sadaukar da rayuwarsa wajen inganta su.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba marigayin hutawa cikin salama.
Rayuwarsa Kafin Shahara
Kafin ya yi suna a masana’antar fina-finai, Ogogo ya yi aiki a matsayin makanike a Ogun State Water Corporation na tsawon kimanin shekaru 13.
Ya fara harkar wasan kwaikwayo a shekarar 1981, inda ya riƙa haɗa aikin wasan kwaikwayo da sana’ar makaniki. Daga bisani, a shekarar 1994, ya bar aikin makaniki gaba ɗaya domin mayar da hankali kan harkar fim da wasan kwaikwayo.