Kamfanin NNPC Limited da abokan hulɗarsa na OML 118 sun rattaba hannu kan muhimman yarjejeniyoyi da za su ciyar da aikin Bonga Southwest/Aparo gaba zuwa matakin yanke shawarar zuba jari na ƙarshe.

A cewar wata sanarwa da Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin, Andy Odeh, ya fitar, ana sa ran aikin zai jawo zuba jari har dala biliyan 21, abin da zai mayar da shi cikin manyan ayyukan hako mai daga teku da aka taɓa gudanarwa a Najeriya.

Ana sa ran aikin zai iya samar da gangar mai har 175,000 a kowace rana a lokacin da ya kai kololuwar samarwa.

Babban Daraktan Gudanarwa na NNPC Limited, Bashir Ojulari, ya ce yarjejeniyar wata shaida ce da ke nuna cewa sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya aiwatar a fannin mai da iskar gas suna fara sauya manufofi zuwa ainihin zuba jari.

Aikin Bonga Southwest/Aparo ya kuma kammala aikin pre-engineering design, yayin da aka riga aka zaɓi kamfanin da zai gina babbar na’urar samar da mai da ke iyo (Floating Production Facility).

Jami’an sun bayyana cewa aikin zai taimaka wajen bunƙasa amfani da kamfanonin cikin gida da ƙara ƙwarewar ’yan Najeriya a fannin mai da gas, tare da samar da guraben ayyukan yi da ƙara kuɗaɗen shiga ga gwamnatin tarayya.

Ana kuma sa ran aikin zai ƙara ƙarfafa matsayin Najeriya a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasashen Afirka wajen samar da man fetur daga rijiyoyin da ke ƙarƙashin teku.