Dan takarar Gwamnan Jihar Kano karkashin jami'ar PDP a zaben 2027 Amb. Muhammad Bello Dalha, ya Kara da cewa, babu wani Abu A Gwamnatin APCn Kano da zai bashi tsoro Domin Gwamna ya kwabsa.


Amb. Dalha yayi wadannan kalamai ne yayin hira da kafar Ammascoradio.


"Kana ganin akwai wanda zai zabi Gwamna abba? Bayan Barnar da ya yi mana a filin Idi da Haj camp da Daula, haryanzu Gwamnatin Kano na biyin kudin daula idan Baka sani ba" inji Amb.


Amb. Muhammad Bello Dalha ya bayyana cewa, Ilimi da inganta harkar kiwon Lafiya da bunkasa kasuwanci sune manyan abubuwan da gwamnatinsa zata sanya a gaba. Yana mai cewa, akwai Shirin Mai karfi cikin hikima da binciken masana da za ayi amfani da Shi a Gwamnatinsa wajen bunkasa rayuwar Mata da kananan yara, inganta Kananan Sana'o'i na mata da kuma buda kofofin aiyukan dagaro da kai ga matasa.


A cewarsa Lokacin Mulkin jam'iyar PDP al'umma kasa da Jihar Kano na walwal, akwai Bunkasar tattalin arziki da saukin rayuwa, Adon haka sune abubuwan da gwamnatinsa zata mayar da karfi akai.