Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa kowane yaro a jihar ya samu damar zuwa makaranta.

Namadi, ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da rabon kayan tallafin karatu ga ɗalibai mata a makarantun sakandare da na gaba da sakandare a garin Jahun.

Ya ce shirin zai taimaka wajen ƙara yawan ɗaliban da ke zuwa makaranta, musamman ’yan mata, tare da rage yawan masu daina zuwa makaranta.

Gwamnan ya ce ilimi na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba, domin yana da muhimmanci wajen gina makomar jihar.

A ƙarƙashin shirin, gwamnati za ta raba tufafin makaranta 48,300, jakunkuna 15,000, kayan tsaftar mata 40,000, kayan rubutu 4,000 da littattafan rubutu 40,000 ga ɗalibai mata.