Tsohon Gwamnan Jihar Gombe kuma Sanatan da ke wakiltar Gombe ta Tsakiya, Muhammad Danjuma Goje, ya bayyana cewa har yanzu yana ci gaba da tuntubar mutane da kuma yin shawarwari kan makomarsa ta siyasa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugabannin siyasa daga jam’iyyun PDP da ADC suna kokarin jawo Sanata Goje zuwa jam’iyyunsu, tare da matsa masa lamba ya sauya sheka, bayan da ya bayyana cewa APC ba za ta ba shi tikitin takara ba.
Da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa a gidansa da ke Gombe ranar Asabar, Goje ya musanta cewa ya sauya sheka zuwa wata jam’iyyar siyasa, inda ya tabbatar da cewa har yanzu yana cikin APC.
“Ban sauya sheka zuwa kowace jam’iyyar siyasa ba. Har yanzu ni mamba ne na APC. Amma nan ba da jimawa ba zan bayyana matakin siyasa na gaba da zan dauka. Don haka, ina rokonku da ku ba shugabanninmu hadin kai kuma ku ci gaba da kasancewa masu biyayya ga jam’iyyar,” in ji shi.
Sanatan, wanda yake wa’adi na huɗu a Majalisar Dattawa, ya bukaci magoya bayansa da su koma yankunansu tare da jiran ƙarin bayani daga gare shi.
Da yake waiwayar kusan shekaru 45 da ya shafe yana cikin harkokin siyasa, Goje ya ce ya tsaya takarar zaɓe sau takwas, tun daga Jamhuriya ta Biyu zuwa yanzu, yana mai cewa ya yi nasara a dukkan zaɓukan da ya tsaya takara a baya, ba tare da ya taɓa faduwa ba.