Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta sanar da hutun Babbar Sallah ga dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na ma’aikatar, Musbahu Aminu Yakasai, ya sanya hannu yau Laraba.
Sanarwar ta bayyana cewa daliban makarantun kwana za su fara hutu daga ranar Asabar 23 ga watan Mayun da muke ciki , sannan su koma makaranta ranar Lahadi 31 ga watan Mayun.
Daliban jeka ka dawo kuwa, za su fara hutun ne daga ranar Juma’a 22 ga watan Mayun, tare da komawa makaranta ranar Litinin 1 ga watan Yuni mai zuwa.