Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, tare da haɗin gwiwar jami’an lafiya da tsaftar muhalli, sun fara bincike kan wasu mutane da ake zargi da sarrafa gurbataccen man gyada a titin Mai Malari Bompai kusa da Ramin Ranji a Birnin Kano.


Shugaban hukumar, Comrade Sa’idu Yahaya, ya ce jami’an hukumar sun kai samame wurin tare da dakatar da ci gaba da sarrafa man har sai an kammala bincike domin kare lafiyar al’ummar Jihar Kano.


Shugaban hukumar ya ce bayan samun sahihan bayanan sirri, jami’an sun kai sumame wurin tare da kama kayayyakin da ake amfani da su, yayin da wasu daga cikin mutanen da aka samu a wurin suka bayyana cewa sabulu suke sarrafawa.


Hukumar ta ce an kai samfurin man gyadan zuwa dakin gwaje-gwaje domin gudanar da bincike, kuma da zarar an kammala za a sanar da al’umma sakamakon binciken.