Gwamnatin jihar Kwara ta buƙaci masu ruwa da tsaki a ɓangaren lafiya da su haɗa kai wajen samar da ingantaccen tsarin aiwatar da kiwon lafiya na zamani domin inganta ayyukan lafiya a faɗin jihar.
Kiran ya fito ne yayin buɗe wani taron kwana uku da aka gudanar a birnin Ilorin kan samar da tsarin aiwatar da shirin lafiya na zamani da ya dace da bukatun jihar Kwara.
Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta jihar, Dakta Taoheed Abdullahi, wanda ya wakilci Kwamishiniyar Lafiya, Amina El-Imam, ya ce taron na da nufin mayar da manufofin lafiya na ƙasa zuwa ayyuka na zahiri da za su dace da halin da ake ciki da bukatun al’ummar jihar.
Gwamnatin ta ce haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da ƙwararru a fannin lafiya zai taimaka wajen gina ingantaccen tsarin kula da lafiya na zamani wanda zai sauƙaƙa samar da ayyukan lafiya cikin sauri da inganci ga al’umma.