Jam’iyyar APC ta bayyana gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, a matsayin dan takarar Sanatan Gombe ta Arewa bayan samun kuri’u masu rinjaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a jihar.


‎Shugaban kwamitin zaben fidda gwani na APC a jihar, Mallam Labiru Musa Kafur, ya ce an gudanar da zaben cikin lumana da gaskiya a dukkan kananan hukumomi 11 na jihar.


‎Haka kuma, tsohon mataimakin kwamishinan ’yan sanda, Mohammed Ahmed, ya zama dan takarar APC na Sanatan Gombe ta Tsakiya.


‎Kwamitin ya tabbatar da cewa duk wadanda suka yi nasara sun cika sharuddan kundin tsarin mulki da na jam’iyyar APC domin tsayawa takara a zaben Sanata mai zuwa.