Rundunar ’Yan Sandan ƙasar nan ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da haɗa baki wajen sace wani dattijo a Jihar Kaduna domin neman kuɗin fansa, tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47.
Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labaran Rundunar, DCP Anthony Okon, ya fitar jiya Talata.
Sanarwar ta ce bincike ya nuna cewa Yusuf Rabo, ya haɗa kai da Musa Adamu da Ali Haruna, wanda shi ne jikan dattijon, domin sace mahaifinsa bisa zargin cewa yana da dukiya da dabbobi masu yawa.
Binciken ya kuma gano cewa an sace dattijon har sau biyu, inda aka karɓi kuɗin fansa naira miliyan biyu a karon farko da kuma naira miliyan huɗu da dubu ɗari biyar a karo na biyu.
Rundunar ta ce ana ci gaba da neman Ali Haruna jikan dattijon da ake zargi na da hannu a lamarin.