Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano, REMASAB, ta hukunta wani mai aikin gini, Alhaji Garzali Sani, kan zuba yashi a kan hanya, lamarin da ya toshe kwalbati tare da lalata magudanan ruwa.
Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Malam Abubakar Ahmad, ya fitar yau Laraba.
Sanarwar ta ce kotun tafi-da-gidanka ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Halima A.B. Wali ta ɗauki matakin ne a ci gaba da aikin sa ido da hukumar ke yi domin tabbatar da bin dokokin tsaftar muhalli a faɗin jihar.
Haka kuma kotun ta gurfanar da gidan man TotalEnergies da ke titin Ahmadu Bello Way, tare da hukunta gidajen abinci da dama a titin gidan Zoo, saboda karya dokokin tsaftar muhalli.