Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ta bayyana cewa ta gayyaci tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar Abdullahi Musa kan zargin cire kuɗi daga albashin ma’aikata.
Shugaban Hukumar, Sa’idu Yahaya ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, a Kano ranar Talata.