Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta tabbata zakaran gasar Premier League ta kasar Ingila na bana, bayan da babban kalubalanta, Manchester City, ta tashi kunnen doki 1-1 a karawarta da kungiyar Bournemouth a daren Talata.
Sakamakon wasan ya kawo karshen jiran shekaru 22 da magoya bayan Arsenal suka yi na sake ganin kungiyarsu ta dauki babban kofin kasar Ingila, tun bayan rabon da su lashe shi tun a kakar wasa ta 2003/2004 karkashin tsohon koci Arsene Wenger.
Manchester City, wacce ke da bukatar samun nasara lallai da lallai a wannan wasan domin ci gaba da fafatawa da Arsenal, ta sha mamaki bayan da kungiyar Bournemouth ta jefa mata kwallo ta farko ta hannun Eli Junior Kroupi a minti na 39. Ko da yake Erling Haaland ya fito da City kunya ta hanyar jefa kwallon daidaitawa a minti na 95 daf da za a tashi daga wasan, hakan bai isa ya hana Arsenal lashe kofin ba.
Wannan canjaras da City ta yi ya bar ta da maki 78 a wasanni 37, yayin da Arsenal ke saman tebur da maki 82, wanda hakan ke nufin babu yadda za a yi City ta iya kama Arsenal ko da saura wasa guda a kammala kakar wasa ta bana.
Yanzu haka dai kocin Arsenal, Mikel Arteta, da yaransa za su iya fita buga wasansu na karshe da Crystal Palace ranar Lahadi ba tare da wani fargaba ba, inda a can ne ake sa ran za su daga kofin zakarun na bana.