Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Tsohon ministan sadarwar Najeriya, Isa Ali Pantami ya fitar a shafinsa na Facebook yau Talata, gabanin gudanar da zaɓen fidda gwani a gwamnoni a ranar alhamis mai zuwa.


Pantami ya ce ya janye ne saboda rashin bin ƙa'idar da ta dace wajen tuntuɓar ƴaƴan jam'iyyar a kan shawarwarin da ta yanke, da kuma rashin samun tabbacin gudanar da sahihin zaɓe.