Aƙalla mutane huɗu ne suka rasa rayukansu sakamakon zanga-zangar adawa da tsadar man fetur da hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar Kenya.
Rahotanni sun bayyana cewa dubban mutane ne suka fito kan tituna a manyan biranen ƙasar domin nuna rashin jin daɗinsu kan matsin rayuwa da kuma ƙarin kuɗin man fetur.
An kuma samu rikici tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro, inda aka yi amfani da barkonon tsohuwa da harsasai wajen tarwatsa masu zanga-zangar a wasu yankuna.
Masu zanga-zangar na zargin gwamnatin shugaban ƙasar, William Ruto da gaza magance matsalolin tattalin arziƙi da hauhawar farashin kayayyaki da ke addabar al’umma.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun nuna damuwa kan yadda jami’an tsaro suka yi amfani da ƙarfi wajen dakile zanga-zangar, tare da kira ga gwamnati ta gudanar da bincike kan mutuwar mutanen.
Sai dai gwamnatin Kenya ta ce tana ɗaukar matakan da za su taimaka wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar da rage dogaro da tallafin man fetur domin samun daidaito a nan gaba.
Zanga-zangar dai ta nuna irin ƙalubalen matsin rayuwa da jama’a ke fuskanta a wasu ƙasashen Afirka sakamakon hauhawar farashi da matsalolin tattalin arziƙi.