Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana cewa dakarunta sun yi nasarar ceto yara bakwai da manya biyu da aka yi garkuwa da su daga wani gidan marayu a watan da ya gabata.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an samu nasarar ceton mutanen ne bayan gudanar da wani dogon aikin bincike da ceto.

Sace mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da zama babban ƙalubale a Nijeriya, musamman a yankunan karkara, inda ‘yan fashi da kungiyoyin masu dauke da makamai ke yawaita kai hare-hare.

A ƙarshen watan Afrilu ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari wani gidan marayu da ba a yi wa rijista ba a jihar Kogi, inda suka sace yara 23 tare da wasu manya.

Ko da yake an ceto yawancin yaran jim kaɗan bayan harin, har yanzu akwai yara bakwai da ba a gano inda suke ba kafin wannan sabon samame na sojoji.

Rundunar ta ce waɗanda aka ceto sun haɗa da samari biyar, yara mata biyu da kuma mata biyu manya, waɗanda ake kyautata zaton matan mamallakin gidan marayun ne.