Ɗan wasan gefe na ƙungiyar RB Leipzig, Yan Diomande, ya amince da sharuɗɗan kashin kansa da Real Madrid kan yiwuwar komawarsa ƙungiyar, bayan da Paris Saint-Germain (PSG) ta janye daga neman sa.
Rahotanni sun ce PSG ta fice daga cinikin ne, lamarin da ya bai wa Real Madrid damar ci gaba da tattaunawa da ɗan wasan na ƙasar Côte d’Ivoire mai shekara 19.
Tun da farko, Liverpool ta nuna ƙwarin gwiwa wajen sayen Diomande, inda ta gabatar da tayin farko na fam miliyan 69 (£69m), amma RB Leipzig ta ƙi amincewa. Haka kuma, an ce PSG ta yi tayin fam miliyan 102.5 (£102.5m), wanda shi ma ƙungiyar ta Jamus ta yi watsi da shi.
Bayan haka, Liverpool ta karkata hankalinta zuwa wasu 'yan wasa, yayin da PSG ta janye daga fafatawar, abin da ya buɗe hanya ga Real Madrid.
Rahotanni kuma na nuna cewa, yayin da tattaunawa kan sabuwar yarjejeniya tsakanin Real Madrid da Vinicius Junior ba ta kai ga cimma matsaya ba, ana kallon Diomande a matsayin wanda zai iya zama madadinsa idan ɗan wasan na Brazil ya bar ƙungiyar.
A gefe guda, Arsenal ma na ci gaba da sa ido kan Diomande, musamman bayan rahotannin da ke cewa har yanzu bai amince da tsawaita kwantiraginsa da RB Leipzig ba.