Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa akalla ’yan Najeriya 98 ne suka mutu sakamakon hare-haren ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu tun daga shekarar 2022.

Haka kuma, gwamnatin ta ce kusan mutum 1,500 aka tilasta musu barin Afirka ta Kudu bayan da aka lalata gidajensu da dukiyoyinsu.

Da yake jawabi a wata ganawa da aka gudanar a Abuja, Ƙaramin Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Sola Enikanolaiye, ya zargi gwamnatin Afirka ta Kudu da gaza kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya da sauran baƙi da ke zaune a ƙasar bisa doka.

Ya bayyana cewa da dama daga cikin waɗanda aka kashe ko suka jikkata mazauna ƙasar ne na halal, tare da yin Allah-wadai da ci gaba da hare-haren ƙyamar baƙi.

Sai dai gwamnatin Afirka ta Kudu ta musanta cewa tana goyon bayan ƙyamar baƙi. Ministan Hulɗar Ƙasa da Ƙasa na ƙasar, Lamola, ya ce an kama wasu da ake zargi da hannu a hare-haren, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.

A ƙarshen ganawar, Najeriya da Afirka ta Kudu sun amince da ƙara ƙarfafa tattaunawa kan batutuwan tsaro da hijira domin kare dangantakar ƙasashen biyu da kuma hana sake aukuwar irin waɗannan hare-hare.