Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi maraba da gurfanar da mutane 24 da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa wata mata a yankin Maraban Jos, inda ta bayyana wannan matakin a matsayin wani muhimmin ci gaba wajen tabbatar da adalci da kuma bin doka da oda.


Haka kuma, gwamnatin ta yaba wa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna kan abin da ta bayyana da gaggawar daukar mataki cikin kwarewa dangane da lamarin.


A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar, Ahmed Maiyaki, ya fitar ranar Talata, gwamnatin ta yi Allah-wadai da tarzoma da kuma daukar doka a hannu mutane suka yi, tare da gargadin cewa duk wanda aka samu da laifin daukar doka a hannunsa zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.


Maiyaki ya ce gwamnatin Gwamna Uba Sani na ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, kuma ba za ta lamunci duk wani mataki na aiwatar da hukunci ba tare da bin ka’idojin shari’a ba, ko da kuwa a karkashin kowace irin hujja ce.


Ya jaddada cewa bin doka da oda shi ne ginshikin tsarin dimokuradiyya, yana mai cewa babu wani korafi, zargi ko zato da zai iya zama hujjar kashe mutum ba tare da bin hanyoyin da doka ta tanada ba.


A cewarsa, wannan lamari ya sake nuna illar daukar doka a hannu da kuma muhimmancin kai rahoton duk wani zargi ko abin da ake zato ga hukumomin tsaro da suka dace, maimakon amfani da tashin hankali.