Ƙungiyar Lazio ta sanar da naɗin tsohon kocin ƙasar Italiya, Gennaro Gattuso, a matsayin sabon mai horas da 'yan wasanta bayan rabuwa da Maurizio Sarri a watan Mayu.
Lazio ta bayyana cewa ta yi maraba da Gattuso tare da nuna kwarin gwiwar cewa gogewarsa da ƙwarewarsa za su taimaka wajen cimma burikan da ƙungiyar ta sa a gaba.
Gattuso, mai shekaru 48, ya taɓa jagorantar Napoli zuwa lashe Kofin Italiya a shekarar 2020. Ya koma Lazio ne bayan ya bar aikin horar da tawagar ƙasar Italiya, wadda ta kasa samun tikitin shiga gasar Kofin Duniya.
A halin yanzu, Italiya ba ta naɗa sabon koci na dindindin ba, inda Silvio Baldini ke jan ragamar tawagar a matsayin rikon ƙwarya. Rahotanni kuma na nuna cewa Roberto Mancini na daga cikin waɗanda ake ganin za su iya komawa matsayin kocin ƙasar.