Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya bayyana cewa da a ce ikon yanke hukunci yana hannunsa shi kaɗai, da ya zai haramta amfani da motoci masu gilashi masu duhu (tinted vehicles) gaba ɗaya a faɗin ƙasar nan.
Ya ce motoci masu gilashi masu duhu na barazanar ga tsaro, kuma masu garkuwa da mutane, ’yan fashi da makami da kuma masu aikata laifin “one-chance” na yawan amfani da su wajen aikata miyagun ayyuka.
Disu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake mayar da martani kan damuwar da Shugaban Nigerian Bar Association, Afam Osigwe (SAN), ya nuna dangane da sabunta lasisin gilashi masu duhu da kuma mayar da tsarin bayar da su wata hanyar samun kuɗaɗen shiga. Duk da haka, ya ce ƙungiyar ba ta da wata matsala da yadda ’yan sanda ke sa ido da kuma tsara amfani da irin waɗannan lasisoshi.
Osigwe ya yi jayayya cewa duk da goyon bayan da NBA ke bayarwa ga sa ido da kulawar ’yan sanda kan lasisin gilashi masu duhu, bai kamata a mayar da tsarin zuwa wata hanyar tara kuɗaɗen shiga ba.
Ya kuma nuna shakku kan wajabcin sabunta lasisin lokaci zuwa lokaci, yana mai cewa da zarar an tattara bayanan mota a cikin kundin bayanai (database), babu wata buƙatar ci gaba da neman sabunta lasisin akai-akai.
Shugaban NBA ɗin ya ƙara da cewa bai kamata a miƙa aikin gudanar da lasisoshin ga kamfanoni masu zaman kansu da ke karɓar kuɗaɗe a madadin ’yan sanda ba.