Batun cire tallafin man fetur na ci gaba da haifar da muhawara mai zafi a Najeriya yayin da ake tunkarar babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027.
Babban ɗan takarar hamayya, Atiku Abubakar, ne ya sake tayar da batun bayan da ya bayyana cewa zai dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Kalaman tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar, waɗanda ya yi a makon da ya gabata, sun ƙara zafafa muhawarar siyasa kan makomar manufofin makamashi da tattalin arzikin Najeriya.
Atiku ya ce dawo da tallafin na daga cikin matakan da zai ɗauka domin rage wa ’yan Najeriya radadin tsadar man fetur da kuma matsin tattalin arzikin da suka biyo bayan cire tallafin.
Sai dai batun ya jawo martani daga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wadda ta kare matakin cire tallafin man fetur da aka ɗauka tun bayan hawan gwamnatin yanzu.
Shugaba Tinubu da kansa ya soki ra’ayin Atiku, yana mai nuna cewa dawo da tallafin zai iya sake jefa gwamnatin Najeriya cikin nauyin kuɗaɗen da ke hana samun damar zuba jari a muhimman fannoni.
Muhawarar ta sake buɗe tambayar ko cire tallafin man fetur shi ne mafita mai ɗorewa ga matsalolin tattalin arzikin Najeriya, ko kuma akwai buƙatar sake fasalin manufofin domin rage wahalhalun da talakawa ke fuskanta.
Yayin da zaɓen 2027 ke ƙara matsowa, ana sa ran batun farashin man fetur, tallafi, tsadar rayuwa da kuma yadda za a tafiyar da tattalin arzikin ƙasa za su kasance cikin manyan batutuwan da za su mamaye yakin neman zaɓe tsakanin jam’iyyun siyasa.