Shugaban Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka (Africa CDC), Dr Jean Kaseya, tare da shugabannin ƙasashen Burundi, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Uganda, sun yi kira ga ƙasashen duniya da su ƙara tallafin kuɗi domin ƙarfafa yaƙi da cutar Ebola.
A wata maƙala da suka wallafa tare, shugabannin sun ce ya zama wajibi a ƙara tallafin kuɗaɗe daidai da saurin yaɗuwar cutar, wadda ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 2,600, tare da kamuwa da sama da 5,500 a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
Sun yi gargaɗin cewa jinkirin samar da kuɗaɗen da ake buƙata na iya kawo cikas ga ƙoƙarin kai magunguna da kayan kariya ga ma’aikatan lafiya da sauran mutanen da ke fuskantar haɗarin kamuwa da cutar.
Shugabannin sun kuma buƙaci ƙasashen da ƙungiyoyin da suka yi alkawarin bayar da tallafi su cika waɗannan alƙawura, waɗanda jimillarsu ta kai kusan dala biliyan 1.3.
Sun ce cika waɗannan alkawura zai taimaka wajen ƙarfafa matakan kariya, inganta ayyukan kiwon lafiya da kuma hanzarta ɗaukar matakan da suka dace domin dakile yaɗuwar Ebola.
Sun jaddada cewa yaƙi da cutar na buƙatar haɗin gwiwar ƙasashen Afirka da ƙasashen duniya, musamman wajen samar da isassun kuɗaɗe, magunguna da kayan aikin da ake buƙata domin kare rayukan jama’a.