A tsawon shekaru, malaman addini sun kasance cikin fitattun muryoyin da al’umma ke saurare a Najeriya, musamman a yankunan Arewa, inda suke da gagarumar tasiri wajen wayar da kan jama’a da tsara tunaninsu kan batutuwan da suka shafi rayuwa da al’umma.
Sai dai duk da wannan tasiri da suke da shi a tsakanin mabiyansu, ba kasafai ake ganin ƙungiyoyin malaman addini suna fitowa fili su bayyana goyon bayansu ga wani ɗan siyasa ko wata jam’iyya ba.
Amma sannu a hankali, wannan yanayin na neman sauyawa, musamman yayin da ake ƙara kusantar babban zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
A ƙarshen makon da ya gabata, wata gamayyar ƙungiyoyin malaman addinin Musulunci daga Arewacin Najeriya ta gudanar da wani taro a Jihar Jigawa, inda ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027.
Wannan mataki ya janyo hankalin jama’a, musamman ganin yadda ƙungiyoyin malaman addini ke da tasiri wajen isar da saƙonni ga ɗimbin mabiyansu a yankin.
Haka kuma, wani lamari da ya ƙara ɗaukar hankali shi ne yadda fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sheikh Musa ya yi nuni da cewa tasiri da martabar Sanata Abdul’aziz Abubakar Yari kaɗai sun isa su taimaka wajen samun goyon bayan Arewacin Najeriya ga Tinubu, tare da ƙara wa jam’iyyar APC damar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Waɗannan maganganu da matakai sun haifar da muhawara mai zafi tsakanin ‘yan Najeriya. Wasu na ganin cewa malaman addini ‘yan ƙasa ne kamar kowa, don haka suna da ‘yancin bayyana ra’ayinsu na siyasa da kuma zaɓar ɗan takarar da suke ganin ya dace.
A gefe guda kuma, akwai masu ganin cewa irin wannan goyon baya daga malaman addini na iya yin tasiri sosai a kan mabiyansu, musamman a yankunan da ake kallon malamai a matsayin manyan masu tasiri wajen tsara ra’ayin jama’a.
Tambayar da ta rage ita ce: Shin shiga harkokin siyasa da bayyana goyon bayan wani ɗan takara daga malaman addini wata dama ce ta amfani da ‘yancin ɗan ƙasa, ko kuwa na iya janyo haɗarin haɗa addini da siyasa fiye da kima?
Yayin da zaɓen 2027 ke ƙara kusantowa, ana sa ran wannan muhawara za ta ci gaba da ƙaruwa, musamman ganin yadda manyan ‘yan siyasa da ƙungiyoyin addini ke fara bayyana matsayinsu kan wanda suke son gani a mulkin Najeriya.