Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi ikirarin cewa Iran ta yi yunƙurin kashe ɗaya daga cikin ’ya’yansa maza biyu, sai dai bai bayyana cikakken bayani kan lamarin ko wane daga cikin ’ya’yansa aka nufa ba.
Netanyahu ya bayyana hakan ne a wata hira ta wayar tarho da tashar talabijin ta Isra’ila, Channel 14, yayin da yake magana kan batun samar da kariyar tsaro ga Gadi Eisenkot, tsohon babban hafsan hafsoshin sojin Isra’ila kuma abokin hamayyarsa a siyasa.
“Wani abin mamaki ya faru. Iran ta kai wa ɗaya daga cikin ’ya’yana hari. Iran ta yi yunƙurin kashe ɗaya daga cikin ’ya’yana,” in ji Netanyahu.
Ya ce lamarin ya nuna muhimmancin samar da cikakkiyar kariya ga manyan ’yan siyasar ƙasar, yana mai cewa kariyar da ake bai wa iyalinsa ba “abin jin daɗi ba ce”.
Netanyahu na da ’ya’ya maza biyu, Yair da Avner, da kuma ɗiya mace. Har yanzu ba a tabbatar da wanda ake zargin an yi yunƙurin kai wa harin ba, ko yaushe da kuma inda lamarin ya faru.
Babban ɗansa, Yair Netanyahu, mai shekaru 35, ya shafe tsawon lokaci yana zaune a Miami, Amurka, tun farkon shekarar 2024, kuma rahotanni sun ce yana ƙarƙashin kariyar hukumar tsaron cikin gida ta Isra’ila, Shin Bet.
Ikirarin na Netanyahu ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan matakin Shin Bet na ƙin samar da jami’an tsaron hukumar ga Gadi Eisenkot, wanda ke neman tsayawa takarar firaministan ƙasar a zaɓen da za a gudanar a watan Oktoba.
Har zuwa yanzu, babu wani cikakken bayani da aka fitar a hukumance kan yadda ake zargin Iran ta yi yunƙurin kai harin, kuma Iran ba ta bayar da martani nan take kan zargin na Netanyahu ba.